1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aski ya zo gaban goshi a zaben Amirka

November 4, 2016

Al'ummar Jamusawa na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da abun da suke fata daga Amirka a zaben shugaban kasar da za a kara tsakanin Hillary Clinton da Donald Trump.

https://p.dw.com/p/2SBnk
Hilary Clinton da Donald Trump
Hilary Clinton da Donald TrumpHoto: picture-alliance/dpa/M.Altaffer/N.Shohov

Mafi yawa daga cikin al'ummar Jamusawa dai na da ra'ayi mabanbanta dangane da 'yan takara guda biyu da ke ci gaba da kalubalantar juna, wadanda kuma ke fatan yin tattaki zuwa fadar gwamnati ta White House bayan samun nasara a zaben na ranar takwas ga watan Nuwamba.Theresa Scholz mai shekaru 85 da haihuwa kuma mai karbar pensho a garin Reutlingen, ta kasance 'yar jam'iyyar masu  ra'ayin mazan jiya mai mulki na CDU tsawon shekaru 50 da suka gabata.

US Präsidentschaft TV Debatte Hillary Clinton und Donald Trump
Hoto: Picture-Alliance/J. Raedle/Pool

" Ta ce Idan aka barni zan so a sake samun Obama,ya san me ya yake yi kuma yana da mutunci. Zan ba da goyon bayana idan har Amirkawa suka amince da wa'adin mulki sau uku. Amma idan har aka zabi Trump, gaskiyya ba ma muradin samun rabin wa'adin mulki. Ina masa kallon ainihin manomi. Akwai alamun Clinton na da mutunci kuma za ta taimaka wa mutane,saboda tana da sassaucin ra'ayi kamar SPD a nan Jamus. Za ta so yin abin da ta yi alkawarin aiwaratwa. "Theresa Scholz kamar wasu Jamusawa dai na ganin cewar, zaben Hillary Clinton na nufin dorewar tsarin na inshora kiwon lafiya. Batun da Donald Trump ya ke shirin kawarwa idan har ya samu nasarar darewa kujerar mulkin Amirka. Akwai alamun tambaya dai dangane da yadda wasu magoya bayansa, wadanda wasu mutane ne masu ilimi da sanin yakamata, suka daukakashi har zuwa wannan matsayi.Duk da cewar Helmut Kopp da ke zama jami'in ba da shawarwari kan harkokin kasuwanci a kusa Frankfurt ba mai goyon bayan Clinton ba ne, ya kasance mai bin yakin neman zaben sau da kafa, kuma a tunaninsa Trump ba shi da amshoshin dukkan tambayoyin da ake masa. ''Ni ba mai goyon bayan Clinton ba ne,sai dai abin tausayi da takaici ne cewar mutanen da yawansu ya kai miliyan 320 ba su da wani zabi face tsakanin tsoho mara basira da dottijuwa mai shekaru 72 da haihuwa. Ya dace a ce dukkaninsu biyu na shirye-shiryen shekarunsu na karshe a duniya, maimakon ba da kamanni kamar 'yan shekaru 50 suna rudin jama'a. Makamancin wannan mahawarace aka yi lokacin takarar McCain a 2008, kuma sun girmeshi da shekaru biyu".