1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aski ya zo gaban goshi a gasar kofin Turai

Suleiman Babayo
July 5, 2021

A wasan neman cin kofin kwallon kafa na kasashen Turai aski ya zo gaban goshi inda kasashe hudu suka rage a matakin wasan kusa da na karshe

https://p.dw.com/p/3w4PQ
EURO 2020 | Ukraine vs England | 2. Tor Kane
Hoto: Alberto Lingria/REUTERS

Yanzu haka kasashen Italiya da Spain da Ingila gami da Denmark sun kai matakin wasan kusa da na karshe a gasar neman cin kofin kwallon kafar kasashen Turai da ke wakana yanzu haka.

EURO 2020 | Ukraine vs England
Hoto: Tolga Akmen/Getty Images/AFP

A ranar Talata ake wasan farko na kusa da na karshe inda Italiya za ta fafata da kasar Spain, yayin da ranar Laraba Ingila za ta kece raini da kasar Denmark. Duk kasashen biyu da suka samu galaba za su kara wasan karshe ranar Lahadi mai zuwa.

A wasan neman cin kofin kasashen Latin Amirka da ke gudana, Brazil ta kai matakin wasan kusa da na karshe inda za ta yi arangama da kasar Peru a ranar Talata. Ita ma kasar Agentina bayan lallasa kasar Ecuador da ci 3-0 ta kai matakin wasan kusa da na karshe inda za ta yi fito na fito da kasar Colombiya ranar Laraba.

EURO 2020 | Ukraine vs England | Tor Henderson
Hoto: Alberto Lingria/REUTERS

A wasan sada zumunta na kwallon kafa da aka kara a Amirka, kasar Mexico ta yi laga-laga da Najeriya da ci 4-0.

Kwamitin kula da gasar Olympics wadda za a gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan, ya bayyana cewa akwai sauye-sauye da za a gudanar kan tsauraran matakan da aka dauka kan gasar da za a yi domin rage irin matakan da aka dauka na yaki da annobar  coronavirus, saboda irin yadda aka samu sassauci kan matakan da aka dauka.