1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fargaban sake mayakan Taliban

Abdul-raheem Hassan
March 7, 2020

Shugaban kasar Afganistan Ashraf Ghani ya ce gwamnatinsa ba ta da niyyar ci gaba da tsare mayakan Taliban, amma akwai fargabar za su koma fagen daga.

https://p.dw.com/p/3Z1cv
Afghanistan Kabul Polizei erscheint nach Schießerei
Hoto: AFP

Amirka ta cimma yarjejeniya da kungiyar Taliban kan tsagaita wuta amma za a saki mutanensu 5,000 da ke rufe kamin shiga tattaunawa da bangarebn gwamnati a ranar 10 ga watan Maris na 2020 a birnin Oslo na kasar Norway.

Shugaba Ghani ya ce gwamnatinsa za ta shira kamin ranar tattaunawar bisa sharadin mayakan su ba da tabbacin kare 'yan kasa da mata da matasa daga hare-hare.