Asarar rai sakamakon yajin aiki a Bangladesh
October 27, 2013A kalla mutane hudu ne rahotanni suka ce an kashe a kasar Bangladesh bayan da 'yan adawar kasar suka fara wani yajin aiki na tsawon sa'o'i sittin don matsin lamba wajen ganin an samar da gwamnatin rikon kwarya ta 'yan ba ruwanmu da za ta sanya ido wajen gudanar zabukan kasar da ke tafe a cikin watan Janairun badi.
Biyu daga cikin mutane da suka rasu dai magoya bayan jam'iyyar Awami League ce wadda ke mulkin kasar kuma sun rasa rayukansu ne bayan da masu goyon bayan yajin aikin da ke goyon bayan jam'iyyar BNP suka far musu, yayin da sauran mutune biyun suka rasu a wata arangama tsakaninsu da 'yan sanda.
Yajin aikin dai yanzu haka ya sanya al'amura a kasar sun tsaya cik, inda makarantu da shaguna da sauraran wuraren kasuwanci musamman a Dhakha fadar gwamnatin kasar suka kasance a rufe.
A ranar Asabar dai ta wayar tarho firaminista Sheikh Hasina ta roki tsohuwar firaministar kasar Khaleda Zia wadda jam'iyyarta ta BNP ke jagorantar yajin aikin da su jingine wannan matsayi da suka dauka sai dai Mrs. Zia din ta ce babu gudu babu ja da baya.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal