Kamaru: Rikici ya barke a yankin Bamenda
April 25, 2019Talla
Barkewar rikicin na zuwa ne a daidai lokacin da Jan Egeland, wani jami'i na Kungiyar bayar da agaji ta kasar Norway, ya ke jan hankulan duniya kan su waiwayi bala'in da jama'ar da rikici ya daidaita a rikicin kasar na fiye da shekaru biyu ke ciki. Daruruwan mutane ne suka tserewa gidajensu inda suka zabi rayuwa cikin dazuka ba kuma tare da samun agaji daga ko ina ba kamar yadda aka saba gani a wasu kasashen duniya da ke fama da rigingimu.
A cewar Egeland jami'in na kasar Norway, da ya kai ziyara yankin da ke fama da tashe-tashen hankulan ya yi kira ga kungiyoyi na agaji da shugabannin kasashen Turai da su dubi halin da rayuwar wadannan mutane ke ciki su tallafa musu.