Anyi garkuwa da fararen hula 4 a Nigeria | Labarai | DW | 04.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi garkuwa da fararen hula 4 a Nigeria

Wasu tsageru da ba a san ko su wanene ba a yankin Niger Delta dake da arzikin man fetur a Nigeria, sunyi garkuwa da wasu yan kasar Phillipines uku a yau juma´ar nan.

Rahotanni sun nunar da cewa tsagerun sun yi awon gaba da mutanen ne akan hanyar su ta zuwa aiki, a tsibirin Bonny dake jihar Rivers.

Idan dai za a iya tunawa ko da a jiya sai da wasu tsageru a birnin Fatakwal suka yi garkuwa da wani bajamushe akan hanyar sa ta zuwa aiki a kamfanin Bilfinger da kuma Berger.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, tuni mahukunta da jami´an tsaro suka dugunzuma neman hanyar ceto wadan nan mutane daga hannun wadanda suka yi garkuwa da sun.

Yankin dai na Niger Delta, yayi kaurin suna wajen yadda tsageru ke yawaita yin garkuwa da ma´aikatan kamfaninnikan dake hakar mai a yankin, bisa neman biyan bukatun su.