Antonio Montero ya bayyana kawo ƙarshen aikin sa a Cote D´ivoire | Labarai | DW | 04.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Antonio Montero ya bayyana kawo ƙarshen aikin sa a Cote D´ivoire

Wakilin Majalisar Dinkin Dunia, mai kulla da harakokin zaɓe a Cote D`Ivoire, Antonio Montero, ya bayyana kawo ƙarshen wa adin aikin sa, a wannan ƙasa.

Montero, yayi yabo, ga ɓangarorin siyasar daban daban na ƙasar a game da sakamakon da su ka cimma, a taron Yamouskouro na ranar talata da ta wuce.

A cikin wannan babar haɗuwa shugaban ƙasa Lauran Bagbo, da madugun yan adawa Allasane Watara, da na yan tawaye Guillaume Sorro,da kuma tsofan shugaban ƙasa Henri Konnan Bedie , bisa jagoranci praministan riƙwan ƙwarya Charles Konnan Banny, sun cimma daidaito, kan abubuwa da dama, da su ka shafi shirye shiryen zaɓen da ake sa ran gudanarwa, a watan oktober mai zuwa.

A watan juli, na shekara ta 2005, Sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya tura Montero a ƙasar Cote D´Ivoire, domin sa iddo, a kan yadda shirye shiryen zaɓe ke gudana.