1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

WHO: Annobar corona ta kusa zama tarihi

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 15, 2022

Darakta janar na Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nunar da cewa, annobar cutar corona da ta tsayar da duniya cak na daf da zuwa karshe.

https://p.dw.com/p/4GsmU
Tedros Adhanom Ghebreyesus | Hukumar Lafiya ta Duniya | WHO
Tedros Adhanom GhebreyesuHoto: Salvatore Di Nolfi/dpa/KEYSTONE/picture alliance

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce a yanzu duniya na cikin gagarumin sassauci na annobar, inda ya kara da cewa da hukumarsa ba ta dauki matakan da suka dace ba da an yi ta samun sababbin nau'ikka na cutar. Kawo yanzu dai, hukumar ta fitar da tsare-tsare shida na dakile annobar da ta hallaka dubban mutane. Sai dai duk da haka hukumar ta yi gargadin cewa annobar ta COVID-19 da cutar kyandar biri na ci gaba da yaduwa a duniya, a dangane da haka har yanzu akwai bukatar taka-tsan-tsan.