Annan ya yi maraba da shawarar tura wata tawagar zabe Iraqi | Labarai | DW | 30.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya yi maraba da shawarar tura wata tawagar zabe Iraqi

Babban sakataren MDD Kofi Annan da sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice sun yi maraba da shawarar da aka yanke ta tura wata tawagar sa ido a zabe mai zanama kanta zuwa Iraqi. Wannan tawagar dai ita zata duba korafe-korafen da ake yi game da tabka magudi a zaben ´yan majalisar dokokin Iraqi da aka gudanar a ranar 15 ga wannan wata na desamba. A cikin wata sanarwa da ya bayar Kofi Annan ya ce tawagar wadda hukumar kasa da kasa mai kula da zabe a Iraqi zata tura, zata yi aiki tsakani da Allah tun ba bu ruwanta da zaben da aka gudanar a wannan kasa. Wakilan ´yan sunni wanda suka sha kaye a zaben na Iraqi, sun yi zargin tabka magudi da aringizon kuri´u a zaben sannan sun yi kira da aka sake gudanar da shi. A martanin da ta mayar da farko bayan zaben hukumar kasa da kasa dake kula da zabuka a Iraqi, ta ce an kamanta gaskiya a zaben ´yan majalisar dokokin.