Annan ya rasu yana da shekaru 80 | Labarai | DW | 18.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya rasu yana da shekaru 80

Tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya rasu. Annan da ke zama sakataren majalisar na bakwai, ya mutu ne a kasar Switzerland bayan gajeriyar rashin lafiya.

Al'ummar duniya musamman na Afirka da suka dimauta da labarin mutuwar tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan na cigaba da aikewa da sakonni ta'aziyya.

Sanarwar data fito daga dattawan Afirka, kungiyar tsoffin shugabannin Afirka da marigayi Nelson Mandela ya kafa, ta ce mutuwar Annan ba asara ce ga Afirka kadai ba, har ma da duniya baki daya.

Cikin alhini, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana Kofi Annan da zama jami'in diflomasiyya da ya janyo wa kasarsa ta asali martaba a idon duniya, tare da bada umurnin sauke tutocin Ghana zuwa rabi, na tsawon mako guda.

Shugabannin Afirka da suka hadar da Uhuru Kenyatta da Cyril Ramaphosa na Afirka ta kudu da shugaban Rasha Vladimir Putin, sun aike da tasu ta'aziyyar zuwa ga babban sakataren MDD Antonio Guterres.

A wannan Asabar din ce Kofi Annan ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin Bern a kasar Switzerland, a cewar sanarwar da ta fito daga gidauniyarsa da ke Geneva.