Za a rantsar da Shugaba Joao Lourenco na Angola a wa'adi na biyu a matsayin shugaban kasa, bayan da ya lashe zaben watan Agustan da ya gaba mai cike da takaddama.
Rahotanni sun nunar da cewa an tsaurarar matakan tsaro a dandalin Praca da Republica mai dimbin tarihi da ke Luanda babban birnin kasar ta Angola, inda za a rantsar da Shugaba Joao Lourenco na jam'iyyar MPLA mai mulki. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa, an hango jagororin babbar jam'iyar adawa daga nesa. Babbar jam'iyyar adawa a Angolan ta UNITA dai, ta yi korafin cewa an dauki matakin jibge dimbin sojoji a warin rantsar da sabon shugaban ksar ne domin a razana mutane. Ita dai jami'iyyar adawar ta UNITA ta sha kaye ne a hannun jam'iyyar MPLA mai mulki ta Shugaba Lourenco.