Angola da Habasha sun dauki hankali sosai | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.09.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Angola da Habasha sun dauki hankali sosai

Takaddama kan sakamakon zaben gama gari a Angola da rashin bayar da fifiko ga rikicin aware na Habasha bayan da hatsin Ukraine ya isa nahiyar Afirka na cikin abubuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi a kai.

Angola Wahlkommission Manuel Pereira da Silva Manico

Shugaban hukumar zaben Angola Manuel Pereira da Silva Manico

Jaridar Neue Zürche Zeitung ta rubuta labari mai taken "Takaddama kan sakamakon zaben Angola.‘Yan adawa sun ki amincewa da ‘yar karamar nasara da jam'iyya mai mulki ta samu".Jaridar ta ce bayan kidayar kuri'u na zaben 'yan majalisar dokokin kasar, wasu sakonni biyu masu adawa da juna sun mamaye shafukan sada zumuntar Angolar da ke yankin Kudu maso yammacin Afirka: jam'iyyar MPLA mai mulki ta wallafa wani faifain bidiyo inda shugaba mai ci João Lourenço ya gode wa 'yan Angola kan sakamakon zaben. A lokaci guda kuma, babbar jam'iyyar adawa ta Unita, ta wallafa hoton dan takararta Adalberto Costa Júnior a shafinta na Instagram a karkashin taken, "Shugaban kasa." Alamar da ke nuna cewa 'yan adawa ba su amince da sakamakon zaben ba.

Bayan kidaya sama da kashi 97% na kuri'un da aka kada, hukumar zaben kasar ta sanar da cewa jam'iyyar MPLA ce ke da rinjayen fiye da kashi 51% na kuri'un, yayin da abokiyar hamayyarta Unita ta samu kashi 44%. Wanda ke nuni da yiyuwar shugaba João Lourenço mai shekaru 68 a duniya zai zarce wa'adi na biyu na shekaru biyar, wanda zai tsawaita mulkin shekaru 47 na jam'iyyar MPLA, tun bayan samun 'yancin kai daga Portugal a 1975.

'Yan adawa da wasu al'ummar kasar sun ji tsoron magudin zabe idan aka yi la'akari da yadda MPLA ke da iko sosai kan tsarin zaben da kuma kafafen yada labarai. A zabukan da suka gabata, a kan dade ana takaddama kan sakamakon zaben. Rabin masu jefa kuri'a kusan miliyan 14 ne suka shiga zaben.

"Yakin da aka yi watsi da shi": in ji Süddeutsche Zeitung 

Äthiopien Amhara | Militär auf der Straße

Dakarun gwamnatin Habasha na ci gaba da sintiri a yankin Amhara

"Ana fada a Habasha, miliyoyin mutane na fuskantar barazana. Amma hankalin duniya ya koma wani wuri" da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung ta ci gaba da cewa, a shafin sada zumunta na Facebook, har yanzu ana iya ganin yadda karamin wurin shakatawa na yara ya kasance kafin bama-bamai su fada a kan shi "Wuri mafi aminci ga yaranku," shi ne taken tallan wurin wasan mai suna "Aljannar yara ta RES" a Mekelle da ke yankin arewacin Ethiopiya. Yanzu haka akalla yara biyu ne suka mutu, sakamakon harba makami mai linzami da wani jirgin yakin sojin saman Habasha ya yi a ranar Jumma'a, kai tsaye a gidan aljannar yaran ya koma jahannama.

Watanni biyar ke nan da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni, amma yanzu ana sake samun harbe-harbe da mutuwa a Habasha. Bangarorin biyu dai na zargin juna da fara fadan. Yakin dai ya fara ne a watan Nuwamban shekarar 2020 da wani hari da kungiyar ‘yan tawayen kabilar Tigrai (TPLF) ta kai a barikin Sojojin Tarayya, kuma nan take Firaaminista Abiy Ahmed ya yi martani. Yakin na kusan shekaru biyu, ya janyo miliyoyin mutane sun gudu, kuma akwai yiwuwar kusan mutane 500,000 sun rasa rayukansu. Sai dai hankalin duniya ya karkakata zuwa wani wurin.

Neue Zürcher Zeitung: Hatsin Ukraine ya isa Afirka

Ukrainischer Weizen für Afrika | Mähdrescher in der Ukraine

A karshen alkamar da Ukraine ke nomawa ta isa kasashen Afirka

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa  sharhi mai taken "Hatsin Ukraine ya isa Afirka" inda ton dubu 23 na hatsi da ke kan hanyarsa zuwa Ethiopiya, inda ake da bukatar gaggawa. Ta ce bayan makonni biyu a cikin teku, babban jirgin "Brave Commander" ya isa tashar jiragen ruwa a Djibouti da safiyar Talata. A cikin jirgin akwai ton 23,000 na hatsi daga Ukraine. Wannan dai shi ne babban jigilar kaya na farko da ya isa yankin kusurwar Afirka tun bayan da Rasha ta mamaye kasar a watan Fabrairu.

A watan Yuli, Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya sun jagoranci cimma yarjejeniya tsakanin Kiev da Moscow wanda ya janye takunkumin da Rasha ta yi wa tashohin dakon kayan. Tun daga wannan lokaci, Ukraine ta sake samun damar fitar da miliyoyin ton na hatsi da taki ta teku. Wannan yana da mahimmanci ga Afirka musamman ma a Gabashin Afirka, inda kashi 90% na alkama da ake shigo da su daga kasashen Ukraine da Rasha ne.

 

Sauti da bidiyo akan labarin