Angela Merkel ta yi gangamin siyasa a Bitterfeld | Siyasa | DW | 30.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Angela Merkel ta yi gangamin siyasa a Bitterfeld

Al'ummar birnin Bitterfeld cibiyar masu goyon bayan jam'iyyar AfD mai kyamar baki sun yi wa Angela Merkel ihu a yayin da take gabatar da jawabi gabanin babban zaben kasar na ranar 24 ga watan Satumba.

A yayin da Jamus ke shirin gudanar da zabe a ranar 24 ga watan Satumba shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta gudanar da wani taron gangami a birnin Bitterfeld da ya kasance cibiyar jam'iyyar masu kyamar baki ta AfD. Merkel ta gamu da kalubale daga magoya bayan jam'iyyar a yayin wannan gangami, amma duk da haka ta gudanar da jawabinta kamar yadda ta shirya. Birnin Bitterfeld na daya daga cikin garuruwan Jamus da aka ragargaza a lokacin yakin duniya na biyu.

Deutschland Wahlkampf CDU Kanzlerin Merkel in Bitterfeld-Wolfen (Reuters/H. Hanschke)

Angela Merkel ta bukaci hadin kan 'yan kasa a yayin gangamin

A daidai lokacin da Rainer Haseloff na jamiyyar CDU kana firimiya na jihar Saxony-Anhalt ya soma jawabi gaban mahalarta gangamin taron inda ya jinjina wa shugabar gwamnatin tare da yi ma ta barka da zuwa taron, wasu da suka kasance magoya bayan jam'iyyar adawa ta AfD, sun kece da ihu suna furta kalaman da ke sukar Merkel kan matakinta na bude kofofin kasar ga dubun dubatan bakin haure da yanzu haka ke watse a duk fadin kasar. Hakan bai hana Merkel gudanar da jawabinta ba kamar yadda ta tsara. Ta kuma jadadda bukatar hadin kan 'yan kasa don ciyar da Jamus gaba.

Deutschland Wahlkampf CDU Kanzlerin Merkel in Bitterfeld-Wolfen Protest (Reuters/H. Hanschke)

Masu adawa da tsarin Merkel na karbar baki sun yi mata ihu

Ana dai hasashen jam‘iyyar ta AfD mai tsatsaurar ra‘ayi za ta iya samun kashi takwas zuwa tara cikin dari na kuri‘un da za a kada a zaben 'yan majalisun dokokin da ake shirin gudanarwa. Jam'iyyar CDU mai mulki ta Angela Merkel ta fuskanci suka matuka musamman kan matakin gwamnati na amincewa da saukar baki 'yan gudun hijra da suka tsere daga kasashensu bisa dalilai na yaki da sauran matsaloli na rashi.

 

Sauti da bidiyo akan labarin