1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban na cigaba da alaka da al-Ka'ida.

June 2, 2020

Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ya baiyana cewa Taliban na ci gaba da karfafa dangantakar da ke tsakaninta  da kungiyar al-Qaeda.

https://p.dw.com/p/3d9l2
Antonio Guterres bei einer Pressekonferenz in Äthiopien
Hoto: AFP via Getty Images

A wani rahoto da ta fitar na baya-bayan nan, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kungiyar Taliban da karfafa dangantaka da ke tsakaninta da kungiyar Al-Qaeda, duk da yarjejeniyar da suka shiga da Amirka cewa Taliban din za ta katse duk wata alaka da ke tsakaninta da dukkanin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Taliban din dai ta fito karara ta karyata zargin, kuma ta baiyana rahoton a matsayin marar tushe balle makama.

Rahoton ya nuna cewa ko ya yinda ake tsaka da yarjejeniya tsakanin Taliban da Amirkan, Taliban din ta cigaba da tuntubar kungiyar al-Qaeda tare da jaddada alakar da ke tsakaninsu.