1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Burkina Faso sun kashe fararen hula

Suleiman Babayo LMJ
April 25, 2024

Wani rahoton kungiyar kare hakkin dan Adam na Human Right Watch ya zargi dakarun kasar Burkina Faso da halaka kauyawa 223 ciki har da yara 56 a wani hari kan mutnane da ake zargi da hada baki da tsageru.

https://p.dw.com/p/4fCFk
Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina FasoHoto: Vincent Bado/REUTERS

Ana zargin sojojin kasar Burkina Faso da halaka kauyawa 223 ciki har da yara 56, a wasu kauyuka da ke yankin arewacin kasar sakamakon wasu hare-hare guda biyu. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch a cikin wani rahoto da ta sake a wannan Alhamis ta ce sojojin sun kashe fararen hula da ake zargi suna hada kai da tsageru masu ikirarin jihadi, yayin da ake fuskantar tashe-tashen hankula tun shekara ta 2015.

Kungiyar ta ce ta yi hira da shaidun gani da ido da wadanda suka tsira daga wannan bala'i da ya faru a shekara ta 2022.

Ita dai Burkina faso da ke yankin yammacin Afirka tana cikin kasashen yankin Sahel da ake samun tashe-tashen hankula na tsageru masu kaifin kishin addinin Islama.