1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaurar tsaro yayin zabe a Iraki

Abdul-raheem Hassan
October 10, 2021

Kusan mutane miliyan 25 ake sa ran za su kada kuri'unsu a zaben, da zimmar kawo sauyin gwamnatin da 'yan kasar ke kuka da rashin adalci. Sai dai akwai fargabar wasu za su kauracewa zaben.

https://p.dw.com/p/41UBR
Irak -  Mustafa al-Kadhimi bei den Parlamentswahlen
Hoto: Khalid Mohammed/AA/picture alliance

Zaben na zuwa ne kwanaki biyu bayan da 'yan kasar suke tunawa da 'yan fafutuka kusan 600 da aka kashe a lokacin zanga-zangar adawa da rashin adalcin shugabannin gwamnati.

Rundunar sojin Iraki ta jibge jami'an tsaro sama da 250,000 don hana aukuwar hare -haren ta'addanci, an kuma rufe filin sauka da tashin jiragen sama da ke Bagadaza har sai bayan zabe. Ana sa ran samun sakamakon farko na zaben a ranar Litinin.

Kasar wacce ta dogara da arzikin man fetur, na fuskantar rikicin siyasa da matsin tattalin arziki mai zafi, matakin da sa 'yan kasar suka fara zanga-zangar gama gari a 2019.