1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaben 'yan majalisa a Senegal

July 31, 2022

Miliyoyin 'yan kasar Senegal na zaben wakilan majalisar kasar a wannan Lahadi, zaben kuma da ke matsayin zakaran gwajin dafi na zaben shugaban kasa da za a yi a nan gaba.

https://p.dw.com/p/4EvDf
Parlamentswahlen im Senegal
Hoto: Leo Correa/AP/dpa

'Yan kasar Senegal  na zaben 'yan majalisar dokokin kasar a ranar Lahadi, zaben kuma da 'yan adawa ke ganin za su hada karfi domin dakatar da take-taken Shugaba Macky Sall na sake neman wani sabon wa'adi.

An dai zabi Shugaba Macky Sall mai shekaru 60 ne a shekara ta 2012 na wa'adin shekaru bakwai na farko kana aka sake zaben sa a wani wa'adin na shekaru biyar a shekara ta 2019.

Ana dai zargin shugaban na shirya wasu dabarun da ke iya kai shi ga neman takara a 2024, ta yanda zai sauya batun wa'adin mulki sau biyu a kasar.

Idan dai 'yan hamayyar suka yi galabar hana jam'iyyarsa rinjaye a majlisar a zaben na yau, ana iya cewa an yi nasara ke nan wajen dama masa lissafin neman takarar wa'adin na uku da yake kitsawa.

Akalla 'yan Senegal din mutum miliyan bakawai ne dai za su kada kuri'unsu a zaben na ranar Lahadi.