Ana zaben shugaban kasa a Mali
July 29, 2018Talla
A wannan Lahadin ne al'umar kasar Mali ke gudanar da babban zabe, inda shugaba mai ci Ibrahim Boubakar Keita ke neman wani wa'adin na biyu na wasu shekaru biyar.
Mali dai na fama da matsalolin tsaro da suka hada da rikicin kabilanci da na masu tsattsauran ra'ayi, da ya kara muni cikin shekaru biyar na mulkin Shugaba Keitan.
'Yan takara 24 ne ke neman shugabancin kasar, a zaben da tuni wasu suka bayyana fargabar iya fuskantar turjiya daga 'yan bindiga.
Akwai dai manyan 'yan kasuwa da kuma wata mace guda da ke cikin jerin wadanda ke neman takarar.
'Yan kasar miliyan takwas ne aka yi wa rajista.
Za kuma a bude rumfunan zabe ne da misalin karfe takwas agogon kasar, a kuma rufe karfe shida na yammaci.