1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaben kasa a Angola

August 24, 2022

A wannan Larabar ce 'yan kasar Angola ke zaben kasa inda ake hasashen takara za ta yi zafi a tsakanin jam'iyya mai ci da kuma ta manyan masu adawa da ta gwamnati.

https://p.dw.com/p/4Fwtp
Angola Wahl 2022
Hoto: António Cascais/DW

Angola na babban zabenta, inda 'yan kasar da suka kai munzalin zabe ke zabar 'yan majalisar dokoki da ma shugaban kasa a wannan rana ta Laraba.

Ana dai ganin zaben na kasar Angola da ke kudu maso yammacin Afirka, zai fi zafi tsakanin dan takarar jam'iyyar da ke mulki ta People's Movement for the Liberation of Angola, MPLA a takaice, da kuma babbar wadda ke adawa ta Unita wadda jagoran tawayen kasar a shekarun baya Jonas Savimbi ya kafa.

Shugaba mai ci João Lourenço, wanda ke mulki a tun shekarar 2017 na neman wa'adi na biyu.

Duk wanda jam'iyyarsa ta samu rinjaye dai a majalisar dokoki, shi ne kai tsaye zai kasance shugaban Angola na gaba.

Babu dai tabbacin samun sakamakon zaben da wuri, abin da wasu ke hasashen zai kwashe kwanaki bayan zabe.