1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Ana fafata wasannin kasashen Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe SB/MA
March 11, 2024

Ghana ta gaza kasancewa a sahun gaba na kasashen da ke lashe lambobi a wasannin motsa jiki na Afirka da take daukar bakunci.

https://p.dw.com/p/4dOv5
Wasannin kasashen Afirka da ke gudana a Ghana
Wasannin kasashen Afirka da ke gudana a GhanaHoto: Fadel Senna/AFP via Getty Images

Wasannin motsa jiki na nahiyar Afirka da ke gudana a biranen Accra da Cape Coast na kasar Ghana sun shiga rana ta uku a hukumance, inda tuni wasu kasashe suka fara kai bantensu ta hanyar lashe lambobi a fannoni da dama. A gasar kokawa ga misali, 'yar Kamaru Blandine Nyeh Ngiri ta samu lambar azurfa a ajin masu nauyin kilo 68. Su ma 'yan Côte d' Ivoire ba a bar su a baya ba, saboda  Celine-Josée Bakayoko Nogona ta lashe azurfa a ajin kilogiram 53, yayin da Amy Youin ta tashi da makamanciyar wannan lamba a ajin nauyiin 76kg a fannin na kokawa. A fannin karate kuwa, kungiyar matan Senegal ta sami lambar azurfa yayin da Makhtar Diop shi ma dan Senegal ya tashi da azurfa a ajin marasa nauyi.

Wasannin kasashen Afirka da ke gudana a Ghana
Wasannin kasashen Afirka da ke gudana a GhanaHoto: Christian Thompson/Matrix Images/picture alliance

A jimlamce dai, Masar ce ke kan gaba da yawan lambobin da suka kai 66 a halin yanzu, ciki har da zinare 36), yayin da Aljeria ke biya mata baya, ita kuma Afirka ta Kudu ke a matsayi na uku. Sai dai babu yabo babu fallassa ga Ghana mai masaukin baki da ta kashe makudaden kudade wajen shirya wasanni na Afirka, inda yanzu haka take a matsaikacin matsayi duk da shan kashi da ta yi a kwallon kafa a gaban Maroko.

Wadannan wasanni na Afirka da ke zama na 13 da aka shirya a wannan nahiya cikin shekaru 49, za su ci gaba da gudana har zuwa ranar 23 ga Maris.  Abin lura a nan shi ne: nasarori a wasu fannoni za su bai wa wasu 'yan wasa damar cancantar shiga gasar Olympics ta birnin Paris daga ranar 26 ga Yuli zuwa 11 ga Agustan 2024.

'Yan wasan Tennis Angelique Kerber
'Yan wasan Tennis Angelique KerberHoto: Alberto Pezzali/AP Photo/picture alliance

A fagen tennis, Bajamushiya Angelique Kerber wacce ta dawo daga hutun haihuwa ta haye mataki na gaba na gasar Indian Wells a Amurka, bayan da ta doke Veronika Kudermetova ta Rasha da ci 6-4, 7-5. Ita dai Kerber da ta lashe Grand Slam sau uku a rayuwarta za ta kara wasanta na gaba ne da Caroline Wozniacki ta Denmark wacce ta taba zama lamba 1 kuma ta dawo daga hutun haihuwa a bazarar da ta gabata. A nata bangaren, tsohuwar ja-gaban tennis ta duniya Naomi Osaka 'yar Japan na wasanta na uku ne Elise Mertens ta Beljiyam watannin kalilan bayan da ta haifi 'ya mace.

A bangaren maza kuwa, duk 'yan tennis da ake ji da su a duniya sun tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar da ke gudana a California ciki har da Carlos Alcaraz da Jannik Sinner da Iga Swiatek da ke zama lamba daya a duniya. Hasali ma cikin sauki ne Iga Swiatek ya yi wajen road da dan Jamhuriyar Czech Linda Noskova da ci 6-4, 6-0, lamarin da zai bai wa Swiatek damar kalubalantar dani Kazakhstan Yulia Putintseva. A nasa bangaren dan Italiya Jannik Sinner da ke a matsayi na uku a duniya ya nuna wa Bajamushe Jan-Lennard Struff da ke a matsayi na 25 cewar ruwa ba sa'an kwando ba ne inda ya doke da shi da ci 6-3, 6-4. Dama dai       Sinner ne ya lashe gasar Australian Open a watan Janairu, kuma ba a doke sa ko sau daya ba a bana.

Yanzu kuma sai nan gida Jamus, inda a karshen mako aka gudanar da wasannin rana ta 25 ta gasar kwallon kafar wannan kasa. kuma har yanzu, taurarin Bayer Leverkusen na ci gaba da haskawa a saman teburi bayan da ta mamaye VfL Wolfsburg da ci 2-0 bayan da aka kori dan wasanta Moritz Jenz sakamakon keta. Sai dai duk da wannan nasarar da ke zama ta 21 a wasannin 25, har yanzu koci Xabi Alonso na Leverkusen na ganin cewar da sauran rina a kaba wajen kafa tarihi na lashe kambun zakara a karon farko.

Duk da taka tsantsan da Alonso ke yo, kungiyarsa ta Leverkusen ta yi wa Yaya-babba Bayern Munich tazarar maki goma. Amma dai a wannan karon Bayern ta yi wa Mainz raba ni da yaro inda ta lallasa ta da ci daya bayan daya har 8-1. Godiya ta tabbata ga dan wasanta na gaba Harry Kane wanda ya ci kwallaye uku, lamarin da ya sa shi cika jimillar kwallaye 30 a kakar wasar Bundesliga a bana, kuma yake fatan ci gaba da zura kwallo har zuwa ranar karshe.

 A nata bangaren, Stuttgart da Sebastian Hoeness ke horaswa ta samu nasara da 2-0 a kan Union Berlin, inda dan asalin Guinea Serhou Guirassy ya sake cin kallonsa da ke zama na 21 a bana. A yanzu dai Stuttgart na a matsayi na uku da maki 53, yayin da Yaya-Karama Borussia Dortmund ke biya mata baya da maki 47 bayaan da ta yi nasara da ci 2-1 a gaban Werder Bremen.

Bundesliga
BundesligaHoto: INA FASSBENDER/AFP

A sauran wasannin kuwa RB Leipzig ta gasa wa 'yar baya ga dangi Darmstadt aya a hannu 2-0, yayin da Frankfurt ta doke Hoffenheim da ci 2-1, ita kuwa Freiburg ta lallasa Bochum da ci 2-1. A nata bangaren Augsburg ta yi wa sabon shiga Heidenheim ci 1-0, yayin da Borussia Mönchengladbach da 1.FC Cologne suka tashi ci 3-3 a karon batta da suka yi.

A gaggauce a wasan manyan gasannin Turai, Bayan sun canjaras biyu, a wannan karon Real Madrid ta yi wa Celta Vigo cin kacar tsohon keke rankacau 4-0, lamarin da ya sa ta ci gaba da yi wa abokan hamayyarta rata a la Liga din kasar Spain. Har yanzu Real na kan gaba da maki 69 inda maki bakwai ke raba ta da Girona da ke a matsayi na biyu, yayin da babbar abokiyar hamayyarta FC Barcelona ke a matsayi na uku da maki 61.

A Premier League kuwa, Liverpool da Manchester City sun yi fafatawa mai zafi ba tare da kaye ba saboda sun tashi ci 1-1. Sai dai Arsenal ta yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da jan ragamar gasar a daidai lokacin da  rage kwanaki goma a zo karshen kakar wasa.  Manyan dawan kwallon kafar Ingila suna gogan kafadar junansu yayin da suka tinkari kwanar karshe, inda Gunners ke saman teburi da maki 64 sakamakon banbancin zura kwallo da ke tsakaninta da Liverpool, yayin da City ke a matsayi na uku da maki 63.

A Italiya kuwa, Kocin Lecce wato Roberto D'Aversa ya kai wa dan wasan gaban Verona dan kasar Faransa Thomas Henry hari bayan da kungiyar ta doke su da ci 1-0 a wasan mako na 28 na gasar Serie A. Rudanin da barke tsakanin 'yan wasa da mahukuntan kungiyoyin biyu ya kai ga  taho-mu-gama tsakanin Henry da D'Aversa, lamarin da ya sa alkalin wasa ya kore su.