Ana tattara sakamakon zabe a Amirka
November 9, 2022Talla
Ana can ana tattara sakamakon zaben tsakiyar wa'adi mai matukar muhimmanci da aka yi a fadin kasar Amirka a ranar Talata.
Sa'o'i gabanin rufe rumfunan zabe, alamu sun nuna cewa da wuya ne a iya bayyana jam'iyya daya tilo da ta samu rinjaye kai tsaye.
Sai dai hasashe na bayyana jam'iyyar Republicans ta tsohon shugaban kasar, Donald Trump a matsayin wacce ke iya samun rinjyen kujeru a majalisar wakilai, duk da cewa ba kai ga ganin samun rinjaye ba kawo yanzu.
A fili yake dai jam'iyyar Democrats ta Shugaba Joe Biden, na iya rasa iko a dukkanin majalisun Amirkar.
Kuma rashin karfin iko ko rinjaye a majalisun biyu, na nufin Shugaba Biden zai rika fuskantar tazgaro wajen iya cimma burin samun kafa dokoki da sauran bukatu a zaurukan duka biyu.