Ana taron koli kan tazarcen Nkurunziza
May 31, 2015Shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka sun hallara a birnin Dar es salam na Tanzaniya da nufin gudanar da taron koli, wanda zai mayar da hankali kacokan da rikicin siyasa da ake fama da shi yanzu haka a kasar Burundi. Wannan kuwa ya zo ne a daidai lokacin da mataimakiyar shugaban hukumar zaben kasar ta Burundi ta gudu daga kasar tare da yin murabus, sakamakon adawa da al'umma ke ci gaba da nunawa game da yunkurin tazarcen shugaban kasa Pierre Nkurunziza.
Sama da wata guda ne dai kungiyoyin fararen hula da kuma 'yan adawan Burundi suka shafe, suna gudanar da zanga-zangar yin Allah wadarai da shirin Nkurunziza na neman wa'adin mulki na uku, lamarin da suka ce ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma a shekarun baya.
A cikin watan Yuni mai kamawa ne dai za a gudanar da zaben kananan hukumomi da kuma na 'yan majalisa, da ma dai na shugaban kasa da na sanatoti. Sai dai shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka na nema shugaba Nkurunziza ya dage wadannan zabuka.