1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na Allah wadarai da kusten majalisa

Abdoulaye Mamane Amadou
January 9, 2023

Kasashen duniya na cigaba da martani kan kutsen da dumbin magoya bayan tshohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro suka yi a harabar majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/4LuPc
Brasilien Brasilia | Bolsonaro Anhänger stürmen Palácio do Planalto
Hoto: Ueslei Marcelino/REUTERS

Da kyar da jibin goshi jami'an 'yan sanda suka kawar da masu boren da ke nuna adawa da samakon zaben kasar da ya ayyana Lula da Silva a matsayin zababben shuagaban kasa.

A gaban dandazon 'yan jarida a al'barkacin ziyarar aiki a Mexico, shugaban Amirka Joe Biden ya ce ya kadu kan yadda masu kutsen suka yi yinkurin karantsaye ga dandalin dimukuradiyya.

Su kuwa shugabannin kasashen China da Rasha da Canada da Italiya da Jamus, sun bi sahun sauran takwarorinsu na kasashen duniya wajen yin Allah wadarai da masu kusten, inda shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kara jaddada goyoyn bayansa ga zababben shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.

A nashi bangare Fafaroma Francis, cewa yayi ya damu da irin nau'ukan tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa da ke faruwa a yankin Amirka, musamman ma na baya bayan nan da suka auku a Peru da Brazil.