1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana sukar Buhari da rashin nada mukamai

Ubale Musa/USUJuly 1, 2015

Tuni dai aka fara kiransa da sunan Baba go slow, ga shugaban tarrayar Najeriya da ke cikin makonsa na biyar da rantsuwa amma har yanzu yake jan kafa ga nada mukamai.

https://p.dw.com/p/1FrRQ
Nigeria Präsident Amtseinführung von Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Mutumin da ya share shekara da shekaru yana ta adawa dai, Muhammadu Buhari a yanzu haka ya kare da kafa gwamnatin shi da mataimakinsa, kana kuma da mashawartansu uku dake da ruwa da tsaki da batun huldarsu da 'yan kasa.

Abun kuma da ya dauki hankali na 'yan kasa dake rabe a tsakanin masu ganin yana nuna alama ta gazawa da kuma masu yi masa kallon wuce gona da iri, a bisa jan aikin da ke gaba a kasar a halin yanzu.

Duk da cewar dai a baya ya yi nasarar share wattani 20 yana fada ana amsawa, a yanzu babbar hujja ta jan kafa a fadar kakakin na gwamnati, na zaman nazari bisa shirgi na kazantar da ke neman wucewa da sanin kowa a kasar a halin yanzu.

Mallam Garba Shehu dai yace da kamar wuya ga Buharin na rufe ido da irin girma na kazanta, da kuma gaza samun hadin kai na magabatan baya.

Rawar ma'aikata ko kuma gudummowa ta ministoci, ko bayan kundin tsarin mulkin kasar da ya tilasta wakilai na jihohi a cikin majalisa ta ministoci, al'adar kasar a can baya na zaman kafuwar man'yan mukamai dama kaddamar da majalisa ta ministoci babu bata lokaci.

Buharin dai bai boye ba ga burinsa na sake daukar akalla wattanni biyu zuwa uku kafin kai wa ga samar da majalisar da ta ke iya taimakawa yakin sauyin na Buhari. Abun kuma da a tunanin Dr Kole Shatimma da ke jagorantar cibiyar kyauta demokaradiya da cigaba ya saba da tunanin talakawa da ke tunanin tasirin nan take.

Tuni dai kasar ta dau dumi cikin karatun ko dama shugaban da ya zamo gwarzon da ya tunkari masu siyasar baya, na zaman damisa ta takardar da bata iya tsorata kowa balle cizo. To sai dai kuma a tunanin Garba Shehun ke zaman rashin adalci ga Buharin.

Abun jira a gani dai na zaman mafita ga 'yan kasar da ke da kishirwar sauyi, da kuma shugaban da ke neman kallo na kwakwaf dama kasar da ke tunanin kusa kaiwa ga gaci.

Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta