Ana shirin yi wa gwamnatin Madrid bore | Labarai | DW | 03.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana shirin yi wa gwamnatin Madrid bore

Majalisar dokokin Kataloniya ta yi kira ga al'umar yankin da su fito su yi zanga-zangar adawa da fara gurfanar da manyan jami'an gwamnatin yankin da mahukuntan Madrid suka yi.

Majalisar dokokin Kataloniya, ta yi kira ga al'umar yankin da su fito su yi zanga-zangar adawa da fara gurfanar da manyan jami'an gwamnatin yankin da mahukuntan Madrid suka yi. A wani sako ta shafin Twitter, majalisar ta ce mahukuntan Madrid ba su isa tilasta mutane masu 'yanci yin shiru ba.

Bayanai na nunin cewa akwai wasu kungiyoyi a Kataloniyar da suka shirya gangamin adawar ranar 12 ga wannan wata na Nuwamba, baya ga wani yajin aiki na gama-gari da gamayyar kungiyoyin kwadago suka kira a ranar takwas ga wata. Kiraye-kirayen dai na zuwa ne yayin da kotun kasar Spaniya ke shirye-shiryen kama tsohon shugaban yankin Carles Puigdemont wanda a halin yanzu yake a kasar Beljiyam.