Ana samun ci gaba a yaki da talauci | Siyasa | DW | 17.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana samun ci gaba a yaki da talauci

Manufofin MDD dangane da karni na 21 na samun goyan baya

Ilimin faramare ga kowa-da-kowa

Ilimin faramare ga kowa-da-kowa

Matsalar ta talauci da karancin abinci mai gina jiki ta dada yin tsamari a cikin shekaru 15 da suka wuce ko da yake a yanzu an fara hangen wasu abubuwa masu ba da kwarin guiwa a daidai wannan ranar da ake bikin zagayowar ranar yaki da talauci ta duniya saboda cikakken goyan bayan da aka fara samu ga shirin MDD na murkushe wannan matsala a cikin sabon karnin nan da muka shiga.

Ana samun karuwar goyan baya ga manufofin MDD dangane da karnin nan na 21, inda aka wayi gari da yawa daga cikin kasashe mawadata sun fara ba da cikakken la’akari ga shawarar bunkasa yawan kudadensu na taimako zuwa kashi 0’7% na jumullar abin da suke samarwa a shekara. A wannan bangaren kasashen Turai na taka muhimmiyar rawa domin cimma wannan buri.

Wannan bayanin dai ya fito ne daga bakin Jeffrey D. Sachs, mai kula da manufofin na MDD kuma darektar cibiyar nazari ta Earth Institute dake jami’ar Columbia a birnin New York. Ya ce akwai alamomin samun kyautatuwar al’amura a cikin wannan karnin na 21 musamman ma sakamakon wayewar da aka yi da gaskiyar cewa tuni dai duniyar ta zama tsintsiya madaurinki daya. Jeffrey Sachs ya kara da cewar maganar ba kawai ta shafi bunkasa yawan kudaden taimakon raya kasashe masu tasowa zuwa kashi 0.7% ba ne, kazalika har da kyakkyawar niyya ta kashe makudan kudi wajen yaki da cutar nan ta zazzabin cizon sauro da bunkasa harkar noma a kasashen Afurka saboda ta haka ne kawai za a yi kandagarkin yake-yake na basasa da tashe-tashen hankula na siyasa da sauran masifun daga Indallahi. Domin kamar yadda masu iya magana su kan ce „Riga kafi Ya fi Magani“.

Ita dai MDD manufofi uku ne ta saka a gaba, wadanda take fatan cimmusu nan da shekara ta 2015. Wadannan manufofi sun hada da kayyade matsalar yunwa da talauci da ba da ilimin faramare ga kowa-da-kowa da daga matsayin mata a harkokin rayuwa ta yau da kullum da kayyade yawan mace-machen yara da mata masu juna biyu hade da tinkarar cututtuka kamarsu kanjamau da zazzabin cizon sauro sai kuma tattalin yanayin kasa da kewayen dan-Adam a hadin kai tsakanin kasashe masu ci gaban masana’antu da masu tasowa. Amma fa muhimmin abu a game da cimma wannan manufa, kamar yadda aka ji daga bakin Wahu Kaara dake daya daga cikin mutanen da aka gabatar da sunayensu domin lambar yabo ta Nobel, shi ne su kansu magabata a kasashen da lamarin ya shafa su nuna halin sanin ya kamata su kuma cika alkawarinsu na ba da hadin kai tare da kakkabe hannuwansu daga cin hanci da karbar rashawa domin tafiyar da mulki na-gari.