Ana mayar da martani kan yarjejeniyar nukiliyar Iran | Labarai | DW | 03.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana mayar da martani kan yarjejeniyar nukiliyar Iran

Shugabannin Iran sun goyi bayan yarjejeniyar nukilya da aka ƙulla da manyan ƙasashen duniya

Ana ci gaba da mayar da martani kan yarjejeniyar nukiliyar Iran da sauran manyan ƙasashe duniya. Sarkin Saudiyya Salman ya shaida wa Shugaban Amirka Barack Obama cewa yana fata yarjejeniyar ƙarshe da aka ƙulla za ta tabbatar da zaman lafiya a yankin da duniya baki ɗaya.Sai dai majalisar tsaron Isra'ila tana nuna adawa da ƙunshin yarjejeniyar tsakanin Iran da manyan ƙasashen duniya, kamar yadda ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya tabbatar. Netanyahu wanda ya kira Shugaba Obama na Amirka ta waya domin jaddada adawa na yarjejeniyar.

Tawogar Iran a wajen tattaunawar ta samu gaggarumar tarba lokacin da suka koma birnin Tehran, inda dubban mutane suka fito da tutocin ƙasar domin nuna murna kan nasarar da aka samu na yarjejeniyar da ta samu karɓuwa a ciki da wajen ƙasar.
A wajen huɗubar sallar Jumma'a Shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei da sauran manyan malaman ƙasar sun goyi bayan yarjejeniyar nukiliyar da manyan ƙasashen duniya.