1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da zabe a Hong Kong

November 24, 2019

An samu ninkin masu kada kuri'a a zaben kananan gundumomi da ke gudana a Hong Kong, zaben da ke gudana karkashin tsauraran matakan tsaro.

https://p.dw.com/p/3TcUP
Hongkong Wahllokal
Hoto: Reuters/M. Djurica

Sama da mutum miliyan biyu suka fita rumfunan zabe a Hong Kong, a wannan rana da ake zaben shugabannin majalisun gundumomi.

Zaben na yau ana ganin shi a matsayin mataki ne na raba-gardamar zanga-zangar da aka kwashe sama da watanni biyar ana yi a yankin.

An dai ga dogon layuka a rumfunan zabe dabam-dabam, yayin da aka baza 'yan sandan kwantar da tarzoma saboda ko-ta-kwana.

Sama da 'yan takara dubu da 100 ne ke naman kujerun wakilci 452 na gundumomin da ke a yankin.

Ya zuwa yanzu dai fiye da mutum miliyan guda ne suka kada kuri'a ya zuwa yanzu, a zaben da ake ganin an samu ninkin masu zabe idan aka danganta da wanda aka yi a baya.