Ana gab da kakkabe kurkunu a duniya | Labarai | DW | 20.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana gab da kakkabe kurkunu a duniya

Wata cibiya a Amirka ta ce alamun cimma cutar kurkunu a fadin duniya na ci gaba da fitowa fili. Sama da mutum miliyan uku ne suka yi ta fama da cutar ta kurkunu a cikin gwamman shekaru da suka gabata.

Wani sabon rahoto kan cutar kurkunu ya ce duniya na gab da kawar da cutar kwata-kwata daga doron kasa. Cibiyar da ke yaki da cutar da ke kasar Amirka, ta ce a baya-bayan nan ne dai aka samu mutum 30 da suka kamu da cutar a kasar Habasha wato Ethiopia, bayan shan wani gurbataccen ruwan gulbi.

Kasar Mali da a baya aka samu cutar a cikinta, ta dauki shekaru biyu yanzu ba tare da labarin matsalar ba, kamar yadda ita Sudan ta Kudu ba a samu labarinta ba. 

Sama da mutum miliyan uku ne cikin kasashen Afirka da na Asiya, suka yi ta fama da cutar ta kurkunu a cikin gwamman shekaru da suka gabata.