1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana farin ciki da sake bude iyakar Najeriya da Kamaru

November 4, 2021

‘Yan kasuwa da matafiya a Najeriya na farin ciki sakamakon sake bude hanyar da ta tashi daga garin Bama zuwa Banki da ma Kamaru da gwamnatin Borno da sojojin kasar suka yi.

https://p.dw.com/p/42aFC
Nigerian army claims to have cleared Mubi of Boko Haram
Dakarun Najeriya da ke aikin sintiri a iyakar Najeriya da KamaruHoto: picture-alliance/dpaD. Yake

Ana sa ran bude wannan hanyar da zai dawo da harkokin rayuwa da na tattalin arzikin kasa, zai kuma inganta zirga-zirga tsakanin al’umma da gwamnatocin kasashen Najeriya da Kamaru. Yankin Bama da Banki wanda ke kan iyakokin Najeriya da Kamaru na daga cikin wuraren da rikicin Boko Haram ya fi shafa musamman tilasta rufe hanyoyin da ke ratsawa zuwa kasashe makwabta.

Wannan hanya ce mai matukar muhimmanci ga harkokin kasuwanci da na rayuwa na kasashe Najeriya da Kamaru da ma Afirka ta tsakiya kuma ta kasance a rufe sama da shekaru 9 saboda tabarbarewar tsaro da hare-haren Boko Haram da ta karbe iko da wuraren kafin jami’an tsaron Najeriya su kwato su.

Ganin an samun sauki hare-hare, kuma harkokin tsaron sun inganta ya sa gwamnatin jihar Borno tare da hadin guiwar rundunar sojojin Najeriya suka bude wannan hanya domin dawo da harkokin kasuwanci da na rauyuwa kamar yadda ya ke a baya.

Niger 61. Jahrestag | Babagana Umara Zulum Gouverneur
Babagana Umara Zulum, Gwamnan jihar BornoHoto: Mohamed Tidjani Hassane/DW

A cewar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya zama dole a bude wadannan hanyoyin in dai ana son a farfado da yankunan daga hali ni ‘ya su da suka shiga a baya, abin da al'umomin yankunan ke ta san barka ganin tsawon shekaru tara ke nan hanyar ke rufe. 

 

Dr Lawan Jafar Tahir, shehin malami a jami’ar jihar Yobe na ganin ba bude hanyoyin dole ne sai an samar da tsaro da zai tabbatar kare rayuwar matafiya a wannan hanya.

Amma a cewar Manjo Janar Christopher Musa, Kwamnadan rundunar yaki da ta’addanci a shiyar arewa maso gabashin Najeriya da aka fi sani da “Operation hadin kai”, jami’an tsaro za su ci gaba da ba da gudummawarsu ta tabbatar da tsaro.

Yanzu haka kuma ‘yan kasuwa da ke bin hanyar Gamboru sun koka da halin da suke ciki inda suka yi kira ga hukumomi kamar haka.