Ana fargaba kan lafiyar Shugaba Bouteflika | Labarai | DW | 21.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana fargaba kan lafiyar Shugaba Bouteflika

An dai tsara cewa Merkel za ta gana da shugaban na Aljeriya a ranar Litinin sai dai rashin lafiyar shugaban ba ta ba shi dama ba.

A ranar Talatan nan a kasar Aljeriya an shiga yanayi na rudani da ma rade-radi kan rashin lafiya da makomar mulkin Shugaba Abdelaziz Bouteflika abin da ke zuwa bayan da shugaban dan shekaru 79 ya dage ganawarsa da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Da fari dai an tsara cewa Merkel za ta gana da shugaban a ranar Litinin a kokarin na ganin wannan kasa da ke a Arewacin Afirka ta taka muhimmiyar rawa wajen hana kwararar baki daga Afirka zuwa Tekun Bahar Rum zuwa nahiyar Turai.

Ofishin Shugaba Bouteflika dai ya bayyana cewa shugaban ba zai samu dama ta ganawa da Merkel ba ne saboda cuta mai nasaba da numfashi, abin da ya sa shugabar ta dage tafiyar da ta tsara yi.

Shugaba Bouteflika dai ya dare karagar mulkin kasar ta Aljeriya tun a shekarar 1999 ya kuma samu cuta da ta shafi rabin jikinsa a shekarar 2013, abin da ke shafar jawabansa da ma sanya shugaban zama a kujerar da ake tura shi. Ba kasafai dai ake ganinsa a bainar jama'a ba, sai dai ya na yawan zuwa Faransa dan duba lafiyarsa.