1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana dakon sakamako a kasar Kwango

December 31, 2018

Wata majalisar malaman addini a Kwango ta yaba zaben kasar da aka yi a ranar Lahadi, zaben da ake hasashen zai sama wa kasar makoma.

https://p.dw.com/p/3AoJy
Kongo hält mit zwei Jahren Verspätung historische Wahlen ab
Hoto: Reuters/O. Acland

Bayan shekaru biyu na kila-wa-kala a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, a karshe an gudanar da zaben shugaban kasa a jiya Lahadi, zaben da kasashen duniya ke sa ran zai sama wa kasar mai fama da rigingimu, sabuwar alkibla.

Majalisar malaman darikar Katholika a kasar, ta ce zaben ya gudana ba tare da gagarumar matsalar da tun da farko aka yi hasashen gani ba.

Sai dai fa bayanai sun tabbatar tashin tashin tashina a wata rumfar zabe a gabashin Kivu ta Kudu, inda ya kai ga mutuwar jami'in dan sanda da baturen zabe gami da wasu mutane biyu.

Kwangon dai a yanzu na gab da mika mulki daga wata gwamnatin zuwa wata, a karon farko tun bayan samun 'yanci daga kasar Beljiyam a shekara ta 1960.

Akwai dai wadanda ke shakkar take-taken Shugaba Joseph Kabila, wanda ya yi kememen mika mulkin a shekarar 2016.