Ana cigaba da ƙidayar ƙuriú a ƙasar Congo | Labarai | DW | 31.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana cigaba da ƙidayar ƙuriú a ƙasar Congo

A ƙasar Jamhuriyar dimokraɗiyar Congo, ana cigaba da ƙidayar ƙuriú, a zaben shugaban ƙasa dana yan majalisun dokoki da aka gudanar a ƙasar a ranar lahadi. Masu lura da harkokin zaɓen daga gamaiyar ƙasa da ƙasa, sun baiyana cewa jamaá sun fito sosai domin ƙaɗa kuriá su. Zaɓen shi ne na farko da aka gudanar lami lafiya a tarihin ƙasar ta tsakiyar Afrika tun bayan da ta sami mulkin kai fiye da shekaru 40 da suka gabata. Dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD su kimanin 17,000 ke sa ido domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen ba tare da wani tashin hankali ba. Shugaban ƙasar mai ci a yanzu Joseph Kabila na kan gaba a jerin yan takara 32 waɗanda ke neman shugabancin ƙasar. Zaá ɗauki tsawon makwanni kafin a sami cikakken sakamakon zaɓen.