Ana ci gaba da samun takaddama kan zaben shugaban kasar Burundi | Labarai | DW | 07.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da samun takaddama kan zaben shugaban kasar Burundi

Shugabannin kasashen Gabashin Afirka sun nemi jinkirta zaben shugaban kasar Burundi

Shugabannin kasashe masu makwabtaka da Burundi sun bukaci jinkirta zaben shugaban kasar da makonni biyu. Haka ya zo yayin da ake fama da tashe-tashen hankula kan shirin Shugaba Pierre Nkurunziza na sake neman mulki a wa'adi na uku.

An tsara zaben shugaban kasar ranar 15 ga wannan wata na Yuli, gwamnatin Nkurunziza tana nuna adawa da shirin jinkirta zaben. Shugabannin kasashen Gabashin Afirka sun nemi a kafa gwamnatin hadin kan kasa. Shugabannin sun nada Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda da ya shiga tsakanin gwamnatin Burundi da 'yan adawa.