1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala zaben shugaban kasa a Kamaru

Zulaiha Abubakar
October 8, 2018

Hukumar zabe a kasar Kamaru na ci gaba da kidaya kuri'u bayan kammala zaben shugaban kasar duk kuwa da cewar 'yan aware sun hana gudanar da zaben a  yankunan dake magana da harshen Ingilishi.

https://p.dw.com/p/3693f
China Peking - Kameruns Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/AP Photo/L. Zhang

Shugaban kasar Paul Biya wanda ke mulkin kasar tun shekara ta 1982 a baya ya dauki alwashin kawo karshen rikicin da yayi sanadiyyar rasa rayuka sama da dari hudu ya bayyana gamsuwarsa da yadda zaben  ya gudana jim kadan bayan ya ka'da kuri'arsa a mazabarsa, yayin da abokin hamayyar sa Joshua Osih daga jam'iyyar SDF mai adawa ya bukaci hukumar zabe tayi adalci wajen kidaya kuri'un,a wani labarin kuma sojoji sun harbe wasu 'yan bindiga a Arewa maso yammacin Bamenda kamar yadda Gwamnan yankin Daben Tchoffo ya shaida wa manema labarai.

Sama da mutane dubu 200 a kasar Kamaru sun rasa muhallansu sakamakon wannan rikici na 'yan awaren yayin  da wasu ke zaman gudun hijira a Najeriya.