Yan kasashen waje na ficewa daga Sudan
April 22, 2023
Talla
Rundunar sojin Sudan ta ce, ta soma kokarin ganin an fitar da jami'an diflomasiya na kasashen yamma daga cikin kasar a yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Khartoum babban birnin kasar. Shugaban kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce, ya bai wa shugabanin kasashen Amirka da Britaniya da Chaina da Faransa tabbacin fitar da 'yan kasashensu daga cikin kasar cikin koshin lafiya.
Mutum sama da dari hudu rahotanni ke cewa, sun mutu a kasar, tun bayan barkewar kazamin fada a tsakanin dakarun sojin Sudan na bangaren shugaban kasar Janar al-Burhan da na shugaban rundunar RSF da Janar Hamdan Dogalo ke jagoranta.