Ana ci gaba da fafatawa a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 06.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da fafatawa a Sudan ta Kudu

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya isa kasar Sudan ta Kudu mai fama da rikici

Dakarun Sudan ta Kudu sun kaddamar da sabon farmakin kan garin Bentiu mai arzikin man fetur, domin sake kwatowa daga hannun 'yan tawaye.

An yi amfani da manyan makamai a wannan Litinin da ta gabata yayin fafatawa tsakanin bangarorin a garin da ke zama helkwatar Jihar Unity. Kasar ta Sudan ta Kudu ta fada cikin rikicin bayan da Shugaba Salva Kiir ya zargi tsahon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnati. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya isa kasar kan neman hanyoyin magance rikicin.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gargadi duk bangarorin biyu su koma teburin sulhu, ko su fuskanci mummunar sakamako.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu