Ana ci gaba da fada a kasar Yemen | Labarai | DW | 19.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da fada a kasar Yemen

An samu asarar rayuka a wani tashin hankali da ya auku a filin jirgin saman birnin Aden na kasar Yemen.

An rufe filin jirgin saman birnin Aden na kasar Yemen biyo bayan wani gumurzu da aka yi tsakanin magoya baya da masu adawa da shugaba Abd-Rabbu Mansur Hadi. rahotanni sun ce an yi asarar rayukan akalla mutane shida sannan fiye da 13 sun jikkata. A kuma halin da ake ciki an bude wuta da bindigogin kakkabo jiragen sama a kan wasu jiragen saman yaki da ba a tantance ba da ke shawagi a sararin samaniyar fadar shugaban kasa da ke kudancin birnin Aden. Wannan ya faru ne bayan an ji karar fashewar wasu abubuwa guda biyu. Mazauna birnin sun ce sun ga hayaki ya tashi a kan wani tsauni inda shugaba Abd-Rabbu Mansur Hadi ya kafa sansaninsa. Sai dai ba a sani ba ko shugaban na wurin.