An zargi ´yan Sunni da hannu a harin da aka kai a Bagadaza | Labarai | DW | 12.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi ´yan Sunni da hannu a harin da aka kai a Bagadaza

FM Iraqi Nuri Al-Maliki ya zargi masu matsanancin ra´ayi na Sunni da magoya bayan tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein da hannu a mummunan harin bam da aka kai kan wata kasuwa da ke Bagadaza. Akalla mutane 60 daukacin su talakawa ´yan shi´a suka mutu sannan fiye da 150 sun jikata lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a motarsa bayan ya tukata cikin wani gungun leburori dake neman aiki a babban birnin na Iraqi. Wanna dai shi ne karo na 4 da kai hari a wannan wuri a cikin wannan shekara kadai.