An zargi ′yan aware da yunkurin juyin mulki a Yamen | Labarai | DW | 28.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi 'yan aware da yunkurin juyin mulki a Yamen

Firaministan kasar Yemen Ahmed bin Daghar a wannan rana ta Lahadi ya zargi masu neman aware daga kudancin kasar da yunkurin kifar da gwamnati.

Jemen Ali Abdullah Saleh wurde ermordet (Getty Images/AFP/M. Huwais)

Mayakan Houthi ke da ta cewa a birnin Sanaa

Wannan dai wani babi ne aka bude a wannan kasa mai fama da talauci tsakanin kasashen Larabawa wacce tuni ma yaki na tsawon shekaru hudu tsakanin gwamnati da ke samun goyon bayan Saudiyya, da 'yan Houthi masu samun goyon bayan Iran ya daidaita kasar.

Firaministan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa da ma juyin mulki ga mahukunta a birnin Sanaa ya yi nisa yayin da kuma aka bude hanyar juyin mulki ga halastacciyar gwamnati a birnin Aden.

Ya kara da cewa babu wani mutum mai gaskiya a Yemen da zai iya rufe bakinsa yayin da ake kara jefa kasarsa cikin rudani.

Daghar dai ya fitar da wannan sanarwar ce yayin da ake gwabza fada da ya jawo hasarar rayukan mutane da dama wasu kuma suka samu raunuka a kudancin birnin Aden inda fadar mulkin kasar ta ke.