An zargi sojin Kamaru da kisan farar hula
March 28, 2019Talla
A cikin wani rahoto da ta wallafa a wannan Alhamis, kungiyar ta HRW ta ce sojojin gwamnatin Kamarun sun yi amfani da karfin da ya wuce kima tare da kona daruruwan gidaje a yankin daga watan Oktoban bara ya zuwa yanzu.
Sai dai rahoton ya ce ba sojojin kasar ta Kamaru ba ne ke da alhakin kisan illahirin mutanen 170, kana su kansu sojojin gwamnatin sun rasa mutane 31 a cikin fadace-fadace sama da 220 da suka wakana a yankin Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma na kasar ta Kamaru a tsukin watannin shida.
Sai dai kuma tuni gwamnatin kasar ta Kamaru ta yi watsi da wannan rahoto na kungiyar ta HRW ta na mai cewa ba shi da tushe balantana makama.