An zargi Siriya da Ƙungiyar IS da aikata laifukan yaƙi | Labarai | DW | 27.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi Siriya da Ƙungiyar IS da aikata laifukan yaƙi

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana hakan a cikin rahoton da hukumar kula da hakkin ɗan Adam ta majalisar ta wallafa a wannan Laraba a birnin Geneva.

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya game da hakin ɗan Adam ya ce dakarun gwamnatin Siriya da mayaƙan adawa na 'yan Jihadi sun aikata manyan laifuka a kan ɗan Adam a cikin yakin basasar ƙasar. Rahoton ya ce dakarun Shugaba Bashar al-Assad sun yi amfani da guba a wasu lamura daban-daban guda takwas a yammacin ƙasar a watannin Afrilu da Mayu. Sai dai bai yi karin bayani ba. Sannan dakarun na Assad na ci gaba da aikata ta'asa ciki har da laifukan yaƙi. Rahoton da ya tattara hirarraki 480 da wasu tarin bayanai ya kuma taɓo batun keta hakkin dan Adam da ƙungiyoyin 'yan Islama suka aikata a Siriya. Kana suna tilasta wa kananan yara daukar makami. Akalla mutane dubu 190 aka kashe a rikicin na Siriya da aka fara a shekarar 2011.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane