1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cin mutuncin baki a Faransa.

Gazali Abdou Tasawa
June 26, 2019

Wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam kimanin 20 sun zargi gwamnatin Faransa da cin mutuncin baki 'yan kasashen ketare da ba su samu mafaka a kasar ba.

https://p.dw.com/p/3L6GL
Frankreich Calais - Flüchtlinge aus dem Sudan
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/G. Orenstein

Wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam kimanin 20 sun zargi a wannan Laraba gwamnatin Faransa da cin mutuncin baki 'yan kasashen ketare wadanda ake tsare da su a cibiyoyin dabam-dabam kafin kwashe su zuwa kasashensu bayan da suka kasa samun takardun mafaka a kasar.

 A cikin wata wasika da suka aika wa ministan cikin gidan kasar ta Faransa Christophe Castaner, Kungiyoyin da suka hada da Cimade da Medecin du Monde da Amnesty International sun bayyana cewa sun samu tabbacin labaran mutane biyu sun kashe kansu wasu kuma na ta faman yajin cin abinci, wasu na kokarin tayar da gobara a cibiyoyin da ake tsare da su a sakamakon munmunan halin da ake tsare da su a ciki.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam din sun yi kira ga ministan cikin gida na kasar ta faransa da ya gaggauta daukar matakan shawo kan wadannan matsaloli. Baki sama da dubu 45 ne dai Faransa ta tsare a irin wadannan cibiyoyi a shekarar da ta gabata.