1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Amirka da Iran da yin misayar fursunoni

June 2, 2020

Gwamnatin Amirka ta yi ahuwa ga Sirous Asgari wanda ta zarga da yunkurin satar bayanan sirrin ya yin da ya ke bincike a wata jami'ar kasar wanda ya sa ta garkame shi tun a shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/3d9FD
55. Münchner Sicherheitskonferenz 2019 | Mohammed Dschawad Sarif, Außenminister Iran
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Hase

 Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya mika sakon murna ga iyalan wani babban masanin kimiyyar kasar farfesa Sirous Asgari da gwamnatin Amirka ta yi wa ahuwa, Amirkar dai ta zargi Asgar din da yunkurin satar bayanan sirrin yayin da yake bincike a wata jami'ar kasar wanda ya sa ta garkame shi tun a shekara ta 2016. Sai dai al'ummar kasar da dama ne ke danganta sakin da aka yi wa farfesa da sakin wasu 'yan Amirka da Iran din ta yi, wato wani abu mai kama da musayar fursunoni, wanda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Abbas Mousavi ya karyata zargin.