An zabi sabon shugaban kasar Pakistan | Labarai | DW | 30.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zabi sabon shugaban kasar Pakistan

'Yan majalisar dokokin kasar Pakistan sun zabi Mamnoon Hussain a matsayin Shugaban kasa na 12.

'Yan majalisar dokokin kasar Pakistan sun zabi Mamnoon Hussain a matsayin Shugaban kasa na 12.

A matsayinsa na dan takaran jam'iyyar PML-N mai mulki, shahararren dan kasuwan Mamnoon Hussein da ya zama sabon shugaban, zai maye gurbin Shugaba Asif Ali Zardari, wanda wa'adin mulkinsa na shekaru biyar ke kawo karshe cikin watan Satumba mai zuwa. Sabon shugaban yana da alaka ta kut-da-kut da Firaminista Nawaz Sharif. Jam'iyyar PPP ta Shugaba Zardari mai barin gado ta kaurace wa zaben, saboda sauyin da aka yi na matsowa da lokacin zaben.

'Yan majalisa na kasa da kuma na yankunan kasar hudu suka gudanar da zaben. Hussain dan shekaru 73 da haihuwa, zai karbi ragamar shugabancin kasar wanda babu wani karfin fada aji, saboda duk karfin na hannun firaminista.

A wani abin da ke zama kalubale ga shugabannin kasar ta Pakistan, mayakan Taliban sun fasa wani gidan yari tare da sakin 'yan fursuna kimanin mutane 250.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu