1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zaɓi mace a matsayin shugabar hukumar WHO

November 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bucn

Majalisar Ɗinkin Dunia,ta zaɓi Margarat Chan, wata yar ƙasar China, a matsayin sabuwar shugabar hukumar Majalisar Dinkin Dunia, mai kulla lahia, wato WHO kokuma OMS.

Wannan zaɓe, da ya ba ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin jama´a mamaki, ya zo daidai lokacin da, Majalisar, ta zargi China, da rashin ɗaukar issasun matakai ga hana yaɗuwar cutar murra tsintsaye, da kuma Sida.

Dr Chan, da ta yi zama shugabar kiwon lahia a Hong Kong, zata hau kujera mulki, a farkon shekara mai zuwa.

Ta kuma yi alƙawarin gudanar da aiki tuƙuru, domin cimma burin samar da lahia ga al´ummomin dunia.