An zaɓi Htin Kyaw a matsayin shugaban ƙasar Myanmar | Labarai | DW | 15.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zaɓi Htin Kyaw a matsayin shugaban ƙasar Myanmar

'Yan majalisun dokoki a ƙasar sun kaɗa ƙuri'a zaɓen sabon shugaban wanda shi ne karon farko da aka zaɓa a ƙarƙashin tsarin demokaradiyya a cikin sama da shekaru 50.

Myanmar Htin Kyaw und Aung San Suu Kyi in Naypyidaw

Htin Kyaw sabon shugaban Ƙasar Myanmar tare da Aung San Suu Kyi

'Yan takara uku ne suka tsaya amma kuma 'yan majalisun suka zaɓi Htin Kyaw na kusa Aung San Suu Kyi. Jamiyyar NLD National League For Democracy ta ba da shawara a zabeshi wanda shi ne jagoranta.Saboda Aung San Suu Kyi, dokar kasar ta haramtama tsayawa takara,a kan dalilin cewar ba yar asilin asar ba ce.