An yiwa Schröder faretin girmamawa a birnin Hanover | Labarai | DW | 20.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yiwa Schröder faretin girmamawa a birnin Hanover

Rundunar sojin Jamus ta gudanar da wani gagarumin bikin girmama shugaban gwamnatin Jamus mai barin Gerhard Schröder a birnin Hanover dake arewacin kasar. Schröder dai shi ne shugaban gwamnatin Jamus na biyu da aka taba yiwa wannan kasaitaccen fareti na girmamawa. Faretin da ake yiwa lakabi da Zapfenreich shi ne mafi daraja na rundunar sojin kasar wato Bundeswehr. Gabanin faretin Schröder ya yi jawabin sa na karshe a matsayin shugaban gwamnati. Schröder ya yi fatan cewa sabuwar gwamnatin kawance tsakanin jam´iyar SPD da ta Christian Union zata ci-gaba da aiwatar da manufofin gwamnati musamman a fannin zamantakewa da na ketare. A ranar talata mai zuwa Schröder zai sauka daga mukamin shugaban gwamnati bayan ya shafe shekaru 7 a ofis. Wadda zata gaje shi wato Angela Merkel ´yar CDU zata kasance mace ta farko da ta taba rike ofishin shugaban gwamnati a Jamus.