An yi watsi da sake dunkule jihar Darfur | Labarai | DW | 23.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi watsi da sake dunkule jihar Darfur

Al'ummar yankin Darfur dake yammaci Sudan sun zabi ci ga ba da zama jihohi biyar maimkon sake hadesu jiha daya.Wannan shi ne sakamkon kuri'ar raba garda ma da aka yi

Hukumar da ta lura da kur'iar raba gardama da aka kada, ita ta bayyana cewar wadande ke son ci gaba da zama yada suke a yanzu sune ke da rinjaye kan masu cewar a sake hadewa jihya daya. Dama dai an yi kuri'ar ne, domin korofin da 'yan tawaye da masu adawa da gwamnatin Sudan suka yi, inda suka ce kamata ya yi a hade Darfur baki da ya su zama jiha guda, maimakon jihohi biyar a yanzu. Gwamnatin Sudan ta raba yankin Darfur izuwa jihohi uku a shekara ta 1994, kana daga bisa aka sake raba lardin ya zama jihohi biyar, bayan barkewar fadan kabilanci tsakanin asalin Larabawa da wadanda ba Larabawa ba. Yan tawaye da suka fadi a wannan zaben sun zargi gwamnatin Khartoum da karkata zaben, sai dai dama 'yan tawayen da jam'iyyu masu adawa da gwamnatin Sudan sun kauracewa kuri'ar raba gardaman.