An yi watsi da janye shirin kiwon lafiyar Obamacare | Labarai | DW | 28.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi watsi da janye shirin kiwon lafiyar Obamacare

'Yan majalisar dattawa na Amirka sun yi watsi shirin kawar da dokar kiwon lafiya ta Obamacare wanda aka shafe shekaru ana cece-kuce a kai.

'Yan majalisar dattawan Amirka sun kada kuri'ar kin amincewa da shirin nan na yin watsi da inshora ta kiwon lafiya a kasar da ake yi wa lakabi da Obamacare wadda masu karami da matsakaicin karfi ke cin gajiya sosai.

'Yan majalisar dai sun kada wannan kuri'a ce da tsakar daren jiya Alhamis inda dukannin 'yan jam'iyyar Democrat da ke adawa suka kada kuri'a ta kin amincewa da janye shirin yayin da 'yan Republican su 49 suka kada kuri'arsu ta amincewa.

USA Washington Senator John McCain

Kuri'ar John McCain na jam'iyyar Republican ta taimaka wajen yin watsi da shirin janye inshorar lafiya na Obamacare

Kuri'un sanatoci 3 na Republican ne dai suka taimakawa 'yan Democrat wajen samun wannan nasara kuma daga cikin wanda suka tallafawa 'yan adawar har da Sanata John McCain da ya bar gadonsa na asibiti inda ya ke jinyar cutar sankarar kwakwalwa don kada kuri'arsa.

Wannan dai wani babban ci baya ne ga jam'iyyar Republican wadda ta shafe shekaru 7 ta na fafutuka wajen ganin an janye wannan tsari na kiwon lafiya a kasar ta Amirka.